Search In this Thesis
   Search In this Thesis  
العنوان
Al`adun zamantakewa tsakanin hausawa da misirawa karkashin llimin zantukan walwalar haeshe =
الناشر
Abdulrahaman Ado ,
المؤلف
Abdulrahaman Ado
تاريخ النشر
2015
عدد الصفحات
190 P. :
الفهرس
يوجد فقط 14 صفحة متاحة للعرض العام

from 132

from 132

المستخلص

A cikin wannan kundin bincike, an kawo bayanai na Kwatancin Zantukan Ilimin Walwalar Harshe masu yin nuni da al’adun zamantakewar rayuwa na aure da haihuwa da mutuwa, a tsakanin Hausawa da Misirawa. An yi wannan bincike da manufar gano dangantakar da ke tsakanin Hausawa da Misirawa. An kasa binciken zuwa fannoni shida. Kashi na farko shimfixa ce ta muqaddima (gabatarwa), wadda a cikinta aka yi bayani a kan ma’anonin wasu kalmomi da suka danganci wannan bincike. Kazalika, an kawo bayanai kan gudanar da bincike da bitar ayyukan da suka gabata da taqaitattun bayanai a kan Hausawa da qasar Hausa da Misirawa da qasar Masar. A babi na farko, an kawo bayanai na zantuka masu nuni da al’adun aure a tsakanin Hausawa da Misirawa. A babi na biyu, an yi bayani a kan zantuka masu nuni da al’adun haihuwa a tsakanin Hausawa da Misirawa. Babi na uku na xauke da zantuka masu nuni da al{u2019}adun mutuwa a tsakanin Hausawa da Misirawa. An kawo kwatancin zantukan al’adun zamantakewa tsakanin Hausawa Da Misirawa, a cikin babi na huxu. A cikinsa, aka kawo kamanci da bambancin zantukan ilimin walwalar harshe na aure da haihuwa da mutuwa. Kazalika, an yi amfani da lambobin da suka wakilci zantukan da aka yi bincike a kai, aka yi amfani da mazubin lissafi, aka fitar da jaddawalai da taswirori, kana aka bayar da bayanai na sakamakon bincike. Daga qarshe, a babi na biyar, an yi bayanai na kammalawar aikin ta hanyar kawo tsokaci da shawarwari da naxewa